Miliyoyin alhazai ciki har da ’yan Najeriya ne suka taru a Dutsen Arfa domin tsayuwa a yayin Aikin Hajjin bana duk da tsananin zafin ranar da ake fama da shi a kasar Saudiyya.
Ministan Aikin Hajji na kasar dai ya shawarci mahajjatan da su kasance a cikin tantinansu tun daga tsakain karfe 10 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma, saboda tsananin zafin rana.
Ko a ranar Lahadi sai da Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasar (NCM) ta yi gargadin cewa zafin zai iya kai wa ma’auni 47, inda ta shawarce su da su dauki matakan kariya.
- Musulman Kudancin Kaduna sun yi taron addu’ar zaman lafiya
- Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano
To sai dai duk da haka, mahajjata maza da mata sun rika yin tattaki daga wurare masu nisa domin taruwa a dutsen domin yin addu’a.
Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin mahajjatan Najeriya, Yusuf Hassan, cewa yana sane da shawarar da aka bayar, amma duk da haka zuciyarsa ba za ta iya natsuwa ba sai yah au dutsen na rahama.
“Na yi wa kaina alkawarin cewa sai nah au Dutse Arafat na yi addu’a a duk lokacin da Allah y aba ni dama. Saboda haka ni burina ya cika,” in ji shi.
Sai dai wakilin namu ya shaida cewa akasarin mahajjatan sun yi amfani da shawarar, inda suka tsaya a cikin tantinan nasu suna karatun alkur’ani da salloli da addu’o’i.
Kazalika, wakilin namu ya ce ya hangi jirage masu saukar angulu na shawagi a sararin samaniya, yayin da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri suna yi wa mahajjatan jagora.
Dutse Arafat dai na da tarihi sosai a Musulunci saboda a nan ne tarihi ya nuna Annabi Muhammad (S.A.W) ya gudanar da hudubarsa ta bankwana.
Daga dutsen ne kuma za su koma Muzdalifa da yamma, su kwana a can, kashegari da safe kuma su fara jifan Shedan.