✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su

Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata .

Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200.

Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata .

Ta tsinci kudin ne da yawansu ya kai Dala dubu biyar, kimanin miliyan takwas da dubu 200 a Naira, idan aka canza a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala daya.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da kuma Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato, Hon. Dayyabu Dauda duk sun tabbatar da faruwar lamarin.

“Ta nuna halin dattaku, gaskiya da rikon amana ta hanyar mayar da Dala dubu biyar din da ta tsinta a masallacin harami ga mai su. Hakika ta nuna halin nagarta da tausayi,” in ji Hon Dayyabu.

A wani labarin kuma, hukumar ta NAHCON ta nuna rashin jin dadinta da yadda daya daga cikin maniyyatan jihar Zamfara ta haihu a Madina a makon nan.

Hukumar ta ce ta yi mamakinn yadda matar ta tsallake duk gwaje-gwajen da ake yi a kokarin hana masu juna biyun da suka kusa haihuwa tafiya.

Sai dai ta ce za ta yi cikakken bincike domin ta gano a ina aka samu matsalar.