Jamus ta bayar da izinin yin gwajinta na farko na wata allurar riga-kafin kamuwa da cutar coronavirus.
Hukumar da ke kula da aikin ce ta sanar da haka ranar Laraba, lamarin da ke ba da damar yin gwajin allurar, wadda kamfani Biontech na Jamus da babban kamfanin harhada magunguna na Amurka Pfizer suka hada, a kan ‘yan Adam.
“Cibiyar Paul-Ehrlich (PEI), ta bayar da izinin gwaji na farko na allurar riga-kafin kamuwa da cutar COVID-19 a Jamus,” inji hukumar ta PEI.
Wannan gwajin, wanda shi ne na hudu da aka bayar da izinin yin irinsa a fadin duniya, “muhimmin mataki ne” na samar da “allurar riga-kafin cikin hanzari”, inji hukumar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito hukumar ta PEI tana cewa, “Amincewa a yi gwajin ta biyo bayan nazari ne a tsanake na hadari da fa’idar da allurar ke da su”.
Yayin gwajin dai za a yi wa wasu “lafiyayyun mutane 200 da suka bayar da kansu wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 55″ nau’uka daban-daban na allurar wadda aka yi ta da sinadarin RNA, sannan a mataki na biyu kuma za a shigo da ”yan sa-kai daga cikin mutanen da suka fi fuskantar hadari.
Daga PEI din har kamfanonin da suka kirkiro allurar riga-kafin ba su sanar da lokacin za a fara gwajin ba, ko da yake kamfanin Biontech ya ce “nan ba da jimawa ba” za a fara kuma “kafin lokacin da muka yi tsammani”.
PEI ta kuma yi ikirarin cewa a watanni kadan masu zuwa za a gudanar da karin gwaje-gwaje a kan alluran riga-kafin cutar COVID-19 a Jamus”.