Shugaban kungiyar Makafi ta Najeriya, Isyaku Adamu Gombe ya ce za a fara gudanar da gasar wasannin makafi ta kasa a shekara mai zuwa.
Shugaban ya ce tun lokacin da ya karbi ragamar kungiyar a watan Janairun wannan shekara ya ware wani sashe da yake kula da farfado da harkokin wasannin makafi.
Ya ce a kokarin da suke na ganin ana damawa da makafi a wasanni a fadin Najeriya da ma a duniya baki daya, sun tuntubi hukumar wasannin Olamfik ta Najeriya za kuma su nemi tattaunawa da hukumar da ke kula da wasannin makafi ta duniya da ke Faransa.
Isyaku ya kara da cewa tuni guragu suka yi nisa wajen wakiltar Najeriya a wasannin kwallon guragu, saboda haka bai ga dalilin da makafi ma ba za su wakilci kasar a nan gaba ba.
Daga cikin wasannin da makafin za su fafata sun hada da na kwallon kafa da na daga karfe mai nauyi da na ninkaya da na guje-guje da sauransu.