✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara amfani da ‘WhatsApp’ wajen karbar haraji a Kaduna

Gwamnati ta ce za a fara amfani da tsarin nan da watanni biyu masu zuwa

Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KADRIS) ta ce za ta fara amfani da dandalin WhatsApp wajen karbar haraji, don saukaka hanyar biyan kudin.

Shugaban Hukumar, Zaid Abubakar ne ya bayyana hakan ranar Laraba, yayin taron tattanawa da aka gudanar tsakanin gwamnati da al’ummar jihar.

An dai shirya taron ne kan hanyoyin samar wa jihar kudin shiga, tsakanin kungiyar Tabbatar da Adalc da Shugabanci yayin Karbar Haraji (TJ&GP), da hadin gwiwar KADIRS suka shirya.

Ya ce dandalin WhatsApp da mutane suka saba amfani da shi zai taimaka wa masu biyan kudin harajin samun saukin zuwa bankuna da sauran wuraren cibiyoyin biyan kudin a Jihar.

Ya kuma ce akwai lambar shaida wacce kai tsaye za ta shiga rumbun adana bayanan biyan, da za su dinga bayar wa ga duk wanda ya biya, baya ga wata lambar waya da za su bayar ga wadanda ba su da wayar da ke iya hawa yanar gizo.

Ya ce karkashin tsarin biyan na wayar hannu, za a iya tura harajin ta banki, a kuma duba adadin da ya kamata a biya, hadi da cirar takardar shaidar biya ta banki da sauransu.

“Dukkanin wadannan tsare-tsare da muka ambata, za su fara aiki ne nan da watanni biyu masu zuwa,” in ji shi.