✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harajin China da Amurka: Mece ce makomar tattalin arziƙin duniya?

Yanzu dai rikici ya ɓarke tsakanin ƙasashen, wanda hakan ke barazana ga tattalin arziƙin duniya.

Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin ƙasashen China da Amurka, yayin da shugaba Donald Trump, ya ƙara wa kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga China haraji zuwa kashi 104.

Wannan matakin ya shafi kayayyaki kamar wayoyin hannu, batir, kayan wasan yara da na’urorin wasanni.

China ta ce ba za ta zuba ido ba

China ta bayyana cewa ba za ta zuba ido ta yi tagumi yayin da ake gallaza mata.

China ta mayar da martani da nata harajin kashi wanda ta ƙada zuwa kashi 34 kan kayayyakin Amurka, inda ta kuma ce tana shirin ƙara wani harajin.

Ta rage darajar kuɗinta (Yuan) domin ƙarfafa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

A lokaci guda kuma, ta fara bincike kan wasu manyan kamfanonin Amurka kamar Google, inda kuma ta ke shirin daƙile wasu muhimman albarkatu.

Masana tattalin arziƙi na gargaɗin cewa wannan rikici zai shafi ƙasashe da dama, musamman na nahiyar Asiya kamar Vietnam da Cambodia, waɗanda harajin zai shafa daga Amurka.

Ana kuma ganin cewa wannan zai iya janyo hauhawar farashin kayayyaki a Amurka da kuma raguwar sayayya daga China.

Wannan ba rikicin haraji ba ne – Ƙwararru

Wasu ƙwararru sun bayyana cewa wannan ba kawai rikicin haraji ba ne, wata gwagwarmaya ce ta nuna iko a harkokin kasuwancin duniya.

Ko da yake tattalin arziƙin China na fuskantar tangarɗa a yanzu, amma masana na ganin tana iya ɗorewa, domin kauce wa nuna rauni ga matakin da Amurka ke kai mata.

A gefe guda kuwa, Amurka na fama da matsin lamba daga ‘yan kasuwa da masu zuba jari da ke jin tsoron sakamakon wannan rikici.

Masana na fargabar lokacin da rikicin zai ƙare

Masana sun bayyana cewa da wuya a san yadda wannan rikici zai ƙare.

Amma ana fatan cewa shugabannin ƙasashen biyu za su zauna tattaunawa domin samun mafita.

Ƙasashen duniya na fargabar cewa idan ba a daidaita ba, rikicin na iya taɓa tattalin arzikin duniya gaba ɗaya.