Gwamnatin Jihar Taraba ta ba da umarnin bude makarantun firamare da sakandare a Jihar ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2020.
Kwamishinan Ilimi a Matakin Farko na Jihar, Johannes Jigem, ya bayar da umarnin bude makarantun a lokacin taron masu ruwa da tsakin a harkar ilimi a jihar.
- Farashin kayan abinci ya fadi a kasuwar Saminaka
- Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Jihar Taraba
- Makarantun tsangaya na kwana za su dauki sabbin dalibai
- Gwamnan Taraba ya raba wa ’yan majalisa jifa-jifai
“Muna umartar dukkannin makarantu da su jingine zangon karatu na uku da bullar annoba ya yi wa cikas.
“Bude makarantun a ranar 21 ga watan Satumba zai zama zangon karatu na farko ne kuma kudin zangon karatun da makarantu za su karba ke nan.
“Gwamnati na ba wa iyaye kwarin gwiwar cewa su tura ’ya’yansu makaranta nan take”, inji kwamishinan.
Ya ce Gwamna Darius Ishaku na umartar dukkannin makarantun su bayar da muhimmanci ga kiyaye matakan kariyar COVID-19.
Jingem ya ce budewar ta kebanci makarantun firamare da sakandare ne kadai, amma bai ce komai game da batun bude manyan makarantu a a Jihar ba.