Gwamnatin Najeriya za ta bai wa kowacce daya daga cikin jihohi 36 na kasar Dala miliyan 20 a matsayin tallafin rage radadin annobar Coronavirus.
Karamin Ministan Kasafi da Tsare-Tsaren Kasa, Clem Agba ne ya bayyana shirin raba kudaden wanda ya ce zai fara gudana daga ranar 30 ga watan Yunin bana.
Sanarwar da Mista Agba ya yi ta ce kowacce jiha za ta karbi wannan kudaden cikin tsawon shekaru biyu.
Sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa, Babban Birnin Tarayya na Abuja kuma zai karbi Dala miliyan 15.
A cewarsa, Gwamnatin tana bukatar amfani da wannan kudade wajen rage radadin da annobar Coronavirus ta haifar ta hanyar tallafa wa talakawa da masu kanana da matsakaitan masana’antu da kananan manoma.