✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka a shekarar nan — Bankin Duniya

Tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa sakamakon sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayyar kasar ke aiwatarwa.

Bankin Duniya ya yi hasashen samun matsaikaciyar bunƙasar kaso 3.6 a tattalin arzikin Nijeriya a tsakanin shekarun 2025 da 2026.

Bankin wanda ya bayyana hakan a cikin rahotonsa na hasashen tattalin arzikin duniya na bana da aka wallafa a jiya Alhamis, ya ce za a samu haɓakar ce sakamakon sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayyar ƙasar ke aiwatarwa.

Rahoton ya ƙara da cewa sauye-sauyen baya-bayan nan da Gwamnatin Nijeriyar ke aiwatarwa sun taimaka wajen bunƙasa ƙwarin gwiwar gudanar da kasuwanci.

Fitattu a cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriyar ke aiwatarwa sune janye tallafin man fetur da kuma kudirorin gyaran dokar harajin da suka janyo cece-kuce.

A cewar Bankin Duniyar “yawan arzikin da Nijeriya ke samarwa, GDP, ya ƙaru da kimanin kaso 3.3 cikin 100 a 2024, inda galibi hada-hadar ɓangaren ayyuka ne ya samar da shi, musamman ɓangarorin hada-hadar kuɗi da harkokin sadarwa.

“Ana hasashen bunƙasar arzikin Nijeriyar ta kara faɗaɗa zuwa kimanin kaso 3.6 cikin 100 tsakanin shekarun 2025 zuwa 2026.

“Sakamakon manufar taƙaita hada-hadar kuɗi ta 2024, ana hasashen raguwar hauhawar farashi sannu a hankali, inda za ta tallafa wa bunkasar bangaren ayyuka, wanda ya kasance babban jigo na samun bunkasar arzikin.”

A cikin rahoton mai taken Global Economic Prospects January 2025, Bankin ya ce “tattalin arzikin yankin hamadar Afirka zai haɓaka da kashi 4.1 a shekarar 2025, da kuma kashi 4.3 a shekarar 2026.”