Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce yara miliyan sama da miliyan 10.4 za su yi mafa da tamowa a Najeria da wasu kasashe a shekarar 2021.
UNICEF ta ce kasashen da yaran za su yi fama da yunwa a 2021 su ne Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Mali, Sudan, Sudan ta Kudu, Yemen, Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (DRC).
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- Za mu yaki hauhawar farashin kayan abinci a 2021 — Buhari
- An kama ma’aikacin lafiyar da ya yi luwadi da mai dauke da COVID-19 a asibiti
“Yayin da shekarar 2021 ke shigowa, UNICEF na ta damu game da lafiya da amincin kananan yara miliyan 10.4 da ake hasashen za su yi yunwa za ta addaba a kasahen a cikin shekarar,” inji hukumar.
Ta ce miliyan 3.3 daga cikin kananan yaran za su yi fama da yunwar ce sakamakon matsalar tsaro da tasirin annobar coronavirus da kuma karancin samun abubuwan more rayuwa.
Sanarwar ta ce a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kadai, yara dubu dari takwas za su yi fama da yunwar da za ta iya ajalin dubu 300 daga cikinsu.
Hukumar ta ce kananan yara miliyan 1.4 ne za su yi fama da yunwa a Sudan ta Kudu a 2021 saboda matsalar rikice-rikice, rashin tsaro, da kuma karancin tsarin kula da lafiya, ruwan sha da lafiyayyen abinci.
Adadin shi ne mafi yawa na yaran da za su tsinci kansu cikin wannan mawuyaicn hali a Sudan ta Kudu tun daga shekarar 2013.
A Jamhuriyar Nijar, Marli da Burkina Faso kuma yaran da za su yi fama da tamowa na iya karuwa zuwa miliyan 2.9 (da kashi 21 cikin 100) sakamkon rikice-rikice, gudun hijira, da sauyin yanayi a kasashen Sahel ta Tsakiya.
Rahoton ya kara da cewa yara miliyan biyu na fama da tamowa a kasar Yemen, kuma adadin na iya karuwa a 2021.
Tun da farko UNICEF ta nemi gudunmuwar Dala biyan daya daga kasashe domin tallafa wa shirinta na samar wa kananan yara da lafiyayyen abinci a kasashen masu rauni a 2021.
Ta kuma yi kira da masu ruwa da tsaki a bangaren jinkai da su fadada bayar da tallafin da ake bayarwa ta bangaren.