Ganin yadda Najeriya ta samu rashin nasara a wasanta da Faransa a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Brazil a ranar Litinin da ta wuce ne ya sa uku daga cikin ’yan kwallon Super Eagles suka yi murabus.
Uku daga cikin ’yan kwallon da suka bayyana wa duniya sun bar yi wa kungiyar wasa su ne Kyaftin Joseph Yobo da Osaze Odemwingie da kuma gola bincent Enyeama.
Joseph Yobo a hirar da ya yi da manema labarai jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin Faransa da Najeriya ya ce lokaci ya yi da zai bar kungiyar Super Eagles bayan ya yi wa kungiyar wasanni 100. Ya ce ganin ya fara tsufa ta sa ya yanke shawarar ba matasa masu tasowa dama don su ma su bayar da tasu gudunmawa a kungiyar. Ya ce wani dalilin yin ritayar tasa shi ne abu ne mai wuya ya sake halartar gasar cin kofin duniya mai zuwa nan da shekaru hudu masu zuwa.
Shi ma Osaze a lokacin da yake hira da wata kafar sadarwa mai suna Mid Zone ya ce ya yi murabus daga kungiyar. “A gaskiya na tsufa, don haka na yanke shawarar yin murabus don na samu damar fuskantar iyalina da kulob din da nake yi wa kwallo a halin yanzu”. inji shi.
Haka shi ma golan Najeriya bincent Enyeama ya ce ya yi ban kwana da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ganin cewa ya fara tsufa.
Idan za a tuna wasu daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles sun rika sukar Enyeama a kan kuskuren da ya yi a wasan Najeriya da Faransa da hakan ta jawo fitar Najeriya daga gasar a ranar Litinin da ta wuce. Duk da wannan kuskure Hukumar FIFA ta tabbatar Enyeama yana daga cikin gololin da suka nuna bajimta a gasar.
Yobo da Osaze da Enyeama sun yi murabus daga Super Eagles
Ganin yadda Najeriya ta samu rashin nasara a wasanta da Faransa a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Brazil a ranar Litinin da…