✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yesu: Mai ceton duniya (4)

Yesu shi ne rai Allah Ya halici mutum da babbar dama –damar yin zabi. Yana da dama ya zabi duk abin da yake so, –…

Yesu shi ne rai

Allah Ya halici mutum da babbar dama –damar yin zabi. Yana da dama ya zabi duk abin da yake so, – ko ya zabi rai da duk abubuwan da rai ke kunshe da su, wato, lafiya, wadata, salama, murna, farin ciki da ire-irensu. Yana kuma da damar ya zabi mutuwa da duk abubuwan da mutuwa ke kunshe da su, wato, la’ana, cuta, kunci, azaba, talauci, kiyayya da ire-irensu.
Da yake Allah haske ne bai taba barin mutum ya yi zabe a cikin duhu ba. Mun gani a rubuce, Ya rigaya Ya shaida wa Adamu irin sakamakon da zai biyo bayan duk irin zabin da zai yi. Nassi yana cewa, “Ubangiji Allah kuma Ya dokaci mutumin, Yana cewa, An yardar maka ka ci daga kowane itacen gona a sake: Amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ba ka ci: cikin ranar da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” Farawa 2:16-17. Wannan ya nuna a fili cewa Adamu bai yi zabi a cikin duhu ba. Yau, duniya tana girbin sakamakon zabin da Adamu ya yi –la’ana, ciwo, hallaka, da kowane irin muguntar da ke akwai; har ya kasance cewa, karshen duk abu mai rai shi ne mutuwa. Wannan mutuwa ba ta tsaya kawai a kan gangar jikin da za a bizne a cikin kasa kawai ba, amma mutuwa ce ta har abada, wato rabuwa da Allah na har abada ke nan.
Har ila yau, bayan da Allah Ya kubutar da ’ya’yan Israila daga kangin bauta domin su zama abin mallakarsa, Ya ba su zabi, Allah Ya ce a cikin Kubawar Shari’a 30:15-16, 19, “Duba a gabanka yau Na sa rai da nagarta, mutuwa da mugunta; da yake ina umurtarka yau ka kaunaci Ubangiji Allahnka, ka bi tafarkunSa, ka kiyaye dokokinSa da farillanSa da shari’unSa, domin ka rayu ka yawaita, domin kuma Ubangijji Allahnka Shi albarkace ka cikin kasa wanda kake shiga ka ci ta… Ina kira sama da kasa su shaida a kanku yau, Na sa rai da mutuwa a gabanka, albarka da la’ana: ka zabi rai fa domin ka rayu da kai da zuriyarka.”
A cikin nasa koyarwa, Yesu ya ba da zabi, nassi yana cewa, “Ana nan a kan rana ta karshe, babbar rana ta idi, Yesu ya tsaya, ya tada murya, ya ce, ‘Idan kowane mutum yana jin kishi, ya zo gare ni, ya sha. Wanda yana ba da gaskiya gare ni, kamar yadda nassin ya fadi, daga cikinsa koguna na ruwa mai-rai za su gudu.” Haka a cikin Ruya ta Yohanna 22:17 Yesu ya sake yin gayyata ga duk wanda ya so, “…Mai jin kishi kuma, bari ya zo; wanda yake so, bari ya diba ruwa na rai kyauta.”
To, Allah dai bai halici mutum domin mutuwa ta mallake shi ba. Mutum ne ya yi wa kansa wannan zabi tun a cikin farkon halittarsa. Zabin da ya yi ta mayar da shi a kan tafarkin mutuwa, da duk zuriyarsa. Littafi Mai tsarki ya shaida mana wannan a cikin Romawa 3:23, “Da yake dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” A cikin Romawa 6:23 aya ta fayyace mana sakamakon zunubi, “Gama sakamakon zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ne cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.”
Mutum dai ba shi da iko ya ceci kansa a ta kowace hanya, ko ta hanyar addini, ibada, addu’a, azumi, sujada, ba da sadaka ko yin hadaya; domin kuwa mutuwa ce take mulki da shi. Nassi yana cewa, ta wurin Adamu mutuwa ta zo kan kowane mutum a Romawa 5:12, ”Domin wannan fa, kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum daya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.”
Tun daga lokacin da Adamu ya zabi tafarkin mutuwa, sai ya zamana cewa duk abin da zai yi zai kai ga mutuwa; domin kuwa mutuwa ce ta mallake shi. Yau a duniya, abubuwan da suke kai mutum ga mutuwa, su suke ta yawaita. Wadannan sun kunshi yake-yake, yunwa, fatara, ta’addanci, kiyayya, cutattuka, haddura, tsoro, fargaba, fashi da sauransu. Idan muka lissabta kwanakin dan Adam a duniya za mu ga cewa duk da bunkasar fasaha da kimiyya raguwa suke ta yi. Wannan kuwa a bayyane yake a cikin Littafi Mai tsarki. Idan muka dubi zamanin da aka yi kafin ambaliyar kwanakin Annabi Nuhu, mutane sun rayu shekaru fiye da dari tara; wanda ya fi dadewa shi ne Metusela wanda ya yi shekara 969 a duniya, Farawa 5:27. Mafi karancin shekaru a wancan zamanin shi ne na Lamec, wanda ya yi shekara 777 a duniya kafin ya mutu, Farawa 5:31. Bayan wadannan sai kwanakin ’yan Adam suka ci gaba da raguwa, domin Allah Ya riga Ya shaida wa Nuhu a Farawa 6:3, ”Ubangiji Ya ce, Ruhuna ba zai rika jayayya da mutum har abada ba, gama shi kuma nama ne: amma kwanakin ransa shekara dari da ashirin za su zama.” Mun gani, Annabi Musa ya mutu yana da shekara 120, kuma sai kwanakin dan Adam ta ci gaba da raguwa, domin Sarki Dauda ya mutu yana da shekara 70.
Yau, a zamaninmu, matasa suka fi saurin mutuwa – su suka fi harbuwa da ciwon kanjamau, su ne da ayyukan ta’addanci, su ne da kunar bakin wake; yawancinsu kuma suna kasa da shekara 30. Me ya kawo duniya ga wannan? Amsa ita ce, mutuwa ce take mulki.
Idan dai ba mutuwa ce take mulki bisa mutum ba, da babu abin da zai sa shi ya kirkiro makaman kare dangi. Gashi a cikin sunan addini, mutane suna ta hallaka rayukan yan Adam; mene ne dalili? Mutuwa tana mulki, sa’annan kuma hallaka tana biye da ita. Mallakar mutuwa a kan mutum ta shafi dukan halittu, shi ya sa yau bala’o’i sai karuwa suke ta yi. Duniya tana ta kokawa da canjin yanayi wanda shi ne sanadin karuwar annoba daban-daban da suka kama daga -girgizar kasa, zaizayar kasa, bijirarrun cutattuka, karancin ruwan sama, tsanantar ambaliyar ruwa, tsananin zafi da tsananin sanyi, gusowar hamada da fari. Hatta kire-kiren kimiyya da fasaha domin kara jin dadin rayuwa ga mutum, su ma sun zame sanadin mutuwa a cikin hanzari. Ga shi komai sai sukurkucewa suke ta yi daga iyawa, sani, gwaninta, kwarewa da ikon mutum. Ina duniya ta nufa ke nan? Amsa, ita ce hallaka, domin kuwa mutuwa ce take mulki. To, akwai mafita ke nan? Ai, rai, shi ne akasin mutuwa. A ina ne mutum zai samu wannan rai wanda zai kayar da mutuwa? Dalilin zuwan Yesu a duniyar tamu ke nan.
Nassi yana cewa, ”A cikinsa akwai rai, rai kuwa hasken mutane ne.” (Yohanna 1:4). Ga abin da Yesu ya shaida game da kansa a Yohanna 14:6, “Yesu ya ce masa : Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai: ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurina.” Yanzu haka Yesu yana jira domin ka gayyace shi ya shigo cikin zuciyarka domin ya ba ka rai na har abada. Ya zo duniya domin ya yantar da mu daga mallakar mutuwa. Me zai hana ka ko ke yin wannan addu’a a cikin natsuwa?
Ya Yesu Almasihu, na yi imani da kai, na gaskanta kai ne mai ceto. Ina rokonka ka shigo cikin zuciyata ka mallake ni. Daga yau ni naka ne zuwa har abada.