✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yayin da tsohon kocin Togo ya rasu

Rahotanni sun ce tsohon kocin kasar Togo dan asalin Brazil, Antonio Dumas ya rasu.  Ya rasu ne a wani asibiti da ke Conakry a  kasar…

Rahotanni sun ce tsohon kocin kasar Togo dan asalin Brazil, Antonio Dumas ya rasu.  Ya rasu ne a wani asibiti da ke Conakry a  kasar Guinea lokacin da yake da shekara 64.

Rahotanni sun ce tsohon kocin ya rasu ne jim kadan bayan ya kamu da rashin lafiya inda aka garzaya da shi wani asibiti a Guinea.

Antonio Dumas ya horar da kasashen Afirka da dama da suka hada da Gabon da Ekuatorial Guinea da Sao Tome da Togo da sauransu.

Ya kafa tarihi a 2002, lokacin da yake horar  da Togo bayan ya gayyaci ’yan kwallon Brazil biyar inda suka buga wa kasar Togo kwallo.

Ya rasu ne a daidai lokacin da yake horar da kulob din AS Kaloum na Guinea. Duk da yake haifaffen Brazil ne amma ya shafe shekaru da dama yana  horarwa a kakasashen Afirka daban-daban har Allah Ya karbi.