Akwai yiwuwar kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Super Eagles ta hadu da kasar Sifen a wasan sada zumunci da Amurka ta shirya.
Hukumar shirya wasan kwallon Amurka ta Major League Soccer (MLS) ce ta shirya wasannin a shirye-shiryen da kasashen duniya ke yi na halartar gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a wannan shekara da muke ciki.
Wasan an yi masa take ne da Shirin Tafiya Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil watau “Road to Brazil” a Turance da ake sa ran kimanin kasashe takwas ne za su fafata a tsakaninsu.
kasashen da ake sa ran za su halarci gasar sun hada da Najeriya da Sifen da Kwaddebuwa da Bosnia-Herzegobina da Honduras da Greece.
Sauran kasashen da za su halarci gasar duk da yake ba su samu hayewa gasar cin kofin duniya ba sun hada da Bolibia da kuma El Salbador.
Wasannin za su gudana ne a tsakanin ranakun 27 ga Mayu zuwa 10 ga Yunin wannan shekara a Amurka.
Sai dai ya zuwa yanzu, babu kasar da ta bayar da tabbacin halartar gasar.
…Yayin da Najeriya za ta hadu da Sifen a wasan sada zumunta
Akwai yiwuwar kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Super Eagles ta hadu da kasar Sifen a wasan sada zumunci da Amurka ta shirya.Hukumar shirya wasan…