Cibiyar Adalci, Ci gaba da Jinƙai ta mabiya ɗarikar Katolika (JDPC) reshen Kafanchan, tare da haɗin guiwar Majalisar Matan Katolika, ta shirya taron horaswa ga shugabannin addini da na gargajiya daga ƙananan hukumomin Jama’a da Zangon Kataf a Kudancin Jihar Kaduna.
Taron, wanda aka gudanar a garin Kafanchan a ƙarƙashin shirin Community Action for Peace and Socio-Economic Development (CAPSED), ya mayar da hankali ne kan zaman lafiya da kuma noma mai ɗorewa, musamman ma yadda ake amfani da takin gargajiya wajen noman citta.
- Kotu ta daure mutumin da yake yada bidiyon tsiraici shekara 76 a kurkuku
- Kotu ta aike da dan TikTok din da ke wanka a kan titi a Kano gidan yari
Taron wanda Hukumar Agajin Katolika ta Ƙasashen Waje (CAFOD) ta ɗauki nauyi na da nufin magance abubuwan da ke haifar da rikici da kuma inganta hanyoyin noma na zamani domin samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a yankin.
A cikin jawabinsa, Rabaran Dakta James Movel Wuye ya jaddada muhimmancin magance mummunan fahimta da ƙyashi tsakanin al’umma.
Ya ce, “Idan muka magance waɗannan matsalolin yadda ya kamata, za mu samu damar rage ƙiyayya da gaba tsakanin ƙabilu da addinai daban-daban a ƙasarmu.” Ya ja kunnen mahalarta game da faɗin kalaman ƙiyayya, yana mai cewa hakan na iya haifar da rikici da kuma cutar da lafiyar ƙwaƙwalwar wanda ake faɗawa hakan.
Da yake jawabi a ɓangaren noma, Dakta Barak Zebedee ya yi bayani ne kan amfani da hanyoyin fasaha wajen gudanar da noma na gargajiya musamman a ɓangaren noman citta. Ya bayyana cewa kakar noma ta shekarar 2023 ta zo da ƙalubale iri-iri na cututtukan citta inda ya shawarci manoma da su rungumi sababbin hanyoyin da ke da kariya daga cutar don samun ribar noma da ɗorewar amfanin gona.
Da yake nasa jawabin tunda farko, shugaban shirin CAPSED, Rabaran Fr. Onuh Ladi, ya bayyana cewa matakin farko na shirin ya samu gagarumin tasiri, musamman wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin mabiya addinai a cikin al’umma.
Ya ce, wannan zagaye na biyu zai ƙara jaddada batun lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma gabatar da sabbin dabarun sasanci ba tare da zuwa kotu ba.
Ya ce, “Manufarmu ita ce, mu ba shugabanni ƙarfin gwiwa da dabarun magance rigingimu cikin gaggawa kafin lamarin ya gagari kundila. A ɓangaren noma kuma, mun ƙarfafa sauya fasalin daga amfani da sinadarai zuwa ga taki na gargajiya, musamman a noman citta,” in ji Fr. Ono.
Ya kuma bayyana cewa, mahalarta za su ci gaba da yaɗawa da koyar da abin da suka koya a cikin al’ummominsu don saƙon ya game sauran manoman da ba su samu damar halartar bitar ba.
Wasu daga cikin mahalarta da suka tattauna da wakilinmu sun nuna godiya da farin ciki da horon da suka samu, inda suka ce ya faɗaɗa fahimtarsu game da koyarwar addinin Musulunci da na Kiristanci kan zaman lafiya da haƙuri. Haka kuma, sun ce zaman ya taimaka musu wajen warware wasu tunanin ba su da tushe a cikin sahihan koyarwar addinansu.