Wata gobara da ba a san musabbabinta ba ta yi sanadiyyar mutuwar wani magidanci mai suna Abdurrahman Abdullahi da aka fi sani da Danjummai, tare da matarsa da ’yar rikonsu.
Aminiya ta ruwaito cewa bayan rasa rayukan mutum uku a gobarar, dakuna uku kowanne ciki da falo sun kone kurmus tare da kayayyakin da ke cikinsu.
- Mutum 3 sun kone kurmus a hatsarin mota a Kano
- Kujerar dan majalisa: Ban gamsu da nasarar NNPP ba, zan tafi kotu – Dan Ganduje
Wani makwabcin magidancin, Abdullahi Maikano, da suka sha da kyar shi da matarsa bayan gobarar ta babbake dakunansu, ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 11 na dare ne gobarar ta tashi.
Ya bayyana cewa matarsa ce ta fara ankara bayan ta jiyo ihun neman taimako, kafin wutar ta hada duka dakuna ukun da ke hagu da daman na makwabtan nasu da suka rasu.
Ya ce da jin ihun maidakinsa, sai ya yi wuf ya fito ya duba, inda ya ga da wutar ta fara haurawa saman dakin su Danjummai.
“Lokacin da wutar ta tsallaka daya makwabtan dakin lokacin masu kawo dauki don kashe wutar sun zo.
“Da sun yi kokarin fasa dakin shi marigayin ne, amma sai suka fara fasa na makwabcinsa, suka fito da yaron da ke ciki, a lokacin wutar ta riga ta mamaye ko’ina a dakin; ta tsallaka har dakinmu da ke daya gefen, inda aka yi ta kawo daukin ruwa ana kashewa.
“Da farko wasu ma tababa ko mutanen cikin dakin sun fita ne, su ma sai bayan an haska ta sama ne aka gano suna ciki,” in ji shi.
Shi ma Mustafa Jibrin, daya daga cikin wadanda suka fara kawo dauki don kashe gobarar ya ce an wahala sosai kafin a fasa kofar da ta ki budewa, inda bayan an yi nasarar fasawa aka tarar da maigidan da matarsa a ciki.
“Mu muka ciccibo marigayin muka fito da shi yana hannuna ina jin yadda yake jan numfashinsa da kyar bai san ma halin da yake ciki ba, bayan kankanin lokaci da fito da shi waje ya cika,” in ji shi.
Sani Abbas, aminin mamacin ne da suka shafe fiye da shekara talatin tare, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda iya mu’amala da mutane tare da riko da addini.
A cewarsa, “Kowane lokaci muna tare da shi kuma tsawon lokacin da muka dauka ba mu taba samun matsala ko wata rigima da shi ba.
“Idan bai gan ni ba zai tambaya ko ya bincika; Kusan ni ne na karshe da muka rabu da shi a daren da abin ya faru; bayan mun yi sallama ya shiga gida ba a yi minti 20 ba lamarin ya faru.”
Marigayin tare da matarsa Zainab ba su taba samun haihuwa ba, amma sun rasu a dakin tare da ’yar ’yar uwarta da take rike da ita tun bayan yaye mai suna Husna.
Jama’a da dama suka halarci jana’izar da aka gudanar a a garin Kafanchan, inda Wakilin Gabas; Alhaji Usman Ibrahim da Hakimin Fada, Alhaji Audi Isa Muhammad da shugaban karamar hukumar Jama’a, Yunana Markus Barde suka kawo ta’aziyya a gidan mamacin da ke layin Jama’a a cikin garin Kafanchan tare da jajantawa ’yan uwan mamatan