✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yayin da Afirka ta Kudu ta yi wa Najeriya kancal a Yamai

kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da U-17 ta kasa kai bantenta na kai wa wasan karshe a…

kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da U-17 ta kasa kai bantenta na kai wa wasan karshe a gasar cin kofin matasa na ’yan kasa da shekara 17 na Afirka da yanzu haka ke gudana a Yamai da ke Nijar, bayan Afirka ta Kudu ta lallasa ta a shekaranjiya da ci 1-0.

Najeriya ce ta zama zakara a gasar cin kofin kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 17 na duniya da ya gudana a Hadaddiyrar Daular Larabawa a shekarar 2013 kuma yanzu ma ta sake hayewa gasar da za a yi a watan Nuwamba a Chile.
Yanzu Najeriya za ta buga wasan neman matsayi na uku ne a tsakanin kasar Mali ko Guinea wadanda suka kara a jiya Alhamis.
kasashe hudu ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 17 da zai gudana a watan Nuwamba a Chile.