✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Ya’yan gidan Sarautar Saudiyya 150 sun kamu da Coronavirus

Sama da ’ya’yan gidan Sarautar Saudiyya 150 ne ake jin sun kamu da cutar Coronavirus da take addabar kasashen duniya a halin yanzu. Jaridar Daily…

Sama da ’ya’yan gidan Sarautar Saudiyya 150 ne ake jin sun kamu da cutar Coronavirus da take addabar kasashen duniya a halin yanzu.

Jaridar Daily Mail Online da ake bugawa a kasar Burtaniya ce ta ruwaito hakan a yau Alhamis inda ta ce hakan ya sa Sarki Salman bin Abdul’aziz da dansa Yarima Mohammed bin Salman sun kebence kansu daga shiga jama’a domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Yanzu haka likitoci a Asibitin Kwararru na King Faisal, wanda nan ne ’ya’yan gidan Sarautar Saudiyya suke jinya, suna ta kokarin samar da karin gadajen kwanciya 500 a wani shirin da suke yi na ko-ta-kwana.

Mahukuntan asibitin sun ce, “Wannan wani umarni ne na shirin karbar manyan mutane daga sassa daban-daban na fadin kasar.”

Wasu biranen Saudiyya ciki har da Riyadh babban birnin kasar suna karkashin dokar ta-baci ta awa 24 da Ministan Cikin Gida ya ayyana. Haka biranen Tabuka da Dammam da Zahran da Hofuf da yankunan Jeddah da Ta’if da Qatif da Khobar suna karkashin dokar.

Yayin daka aka killace birane mafiya tsarki a Musulunci wato Makka da Madina, lamarin da ke kawo fargabar hana gudanar da Aikin Hajjin bana.

%d bloggers like this: