✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawon duniya 2

Wani ne ya bar gida, ya tafi nisan duniya neman kudi, yana da mata marainiya ba uwa ba uba, duk sun mutu sai ya dawo…

Wani ne ya bar gida, ya tafi nisan duniya neman kudi, yana da mata marainiya ba uwa ba uba, duk sun mutu sai ya dawo gida bai samo komai ba duk da ya dade can. Sai matar ta ce: “Maigida maraba, ina ka je ne?” Sai ya ce mata: “Na je lahira!” Sai ta ce: “Ashe ka hadu da iyayena?” Sai ya ya ce mata: “Ai ba ta hanyar ’yan wuta na biyo ba!”
Daga Nafisa U. Kirmitsi, 08036950708