✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja

Babu wanda zai iya cewa ga musabbabin mutuwarsa, amma ’yan kasuwa sun shaida  cewa, an tsinci gawarsa da safiyar ranar Juma’a a babbar ƙofar shiga…

An tsinci gawar wani tsoho mai suna Haruna Abdullahi mai shekara 75 daga garin Gumel na Jihar Jigawa a ƙofar babbar kasuwar Kure Ultra Modern Market da ke Minna a Jihar Neja.

Babu wanda zai iya cewa ga musabbabin mutuwarsa, amma ’yan kasuwa sun shaida wa Daily Trust  cewa, an tsinci gawarsa da safiyar ranar Juma’a a babbar ƙofar shiga kasuwar.

Kakakin rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.

Ya ce, “A yau Juma’a 18/4/2025 da sanyin safiya, an tsinci gawar wani wanda aka bayyana sunansa da Haruna Abdullahi mai kimanin shekara 75 a ƙofar shiga kasuwar Kure.

“An ce mabaraci ne, kuma Bahaushe ne, ɗan jihar Gumel ne, kuma ba a ga wani alamar tashin hankali ba a jikinsa, an kai shi asibiti aka tabbatar da mutuwarsa.”