Mutanen da ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja.
Mazauna yankin sun kuma ce babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya da ta bi ta yankin ita ma ambaliyar ta yanke ta.
Kodayake dai har yanzu babu cikakkun bayanai a kan ambaliyar, amma mazauna yankin sun kiyasta cewa mutanen da suka rasa ransu za su kai 50.
- NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu?
- ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su
Gidaje da sauran kadarori na miliyoyin nairori ne dai suka salwanta, yayin da wasu mazauna yankin kuma ke cewa adadin wadanda suka rasun ma zai iya wuce 50, sakamakon har yanzu akwai mata da kananan yara da dama da ba a san inda suke ba.
Aminiya ta gano cewa ambaliya ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka na tsawon sa’o’i a daren Laraba, inda ya cinye gidaje yayin da mutane suke tsaka da barci.
Wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Usman, a ce tuni har an tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwa, amma har yanzu akwai wadanda ba a kai ga gano su ba, musamman a wuraren da gidajen suka nitse baki daya.
Daraktan Yada Labarai na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar ambaliyar ga Aminiya.
Ya ce har yanzu hukumar na kan aikin tattara bayanai da alkaluma kafin ta kai ga sanar da abin da ta gano.