Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura.
Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi.
- PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike
- Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “A ranar 17/4/2025 da misalin ƙarfe 2:00 na rana, an samu labarin cewa wasu gungun mutane ƙarƙashin jagorancin wani Alhaji Yikangi na ƙauyen Chikan ta hanyar Lemu sun kai hari kan wani Muhammad Ma’aba na ƙauyen Fujeregi, dukkansu a ƙaramar hukumar Gbako.
“An samu rahoton cewa wanda aka kashe ɗin an yi masa dukan tsiya ne saboda rashin fahimtar da wata mata Fatima Suleiman da suke cikin yanki ɗaya, ya mutu a hanyar zuwa babban asibitin Lemu, inda aka tabbatar da mutuwarsa.”
Abiodun ya ƙara da cewa, ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika.