Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da aka samu da laifi a jihar za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Okpebholo ya bada tabbacin a shirye yake ya sanya hannu akan sammacin kisa na waɗanda aka yankewa hukunci a jihar idan kotu ta same su da laifi.
Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Uromi, inda ya tattauna da shugabanni da ’yan uwa na yankin unguwar ’yan Arewa mazauna Esan.
“Ku tuna cewa Majalisar Dokokin Jihar Edo (EDHA) ta zartar da wani ƙudiri na gyara dokar hana garkuwa da mutane (da wasu dokoki da suke da alaƙa da na shekarar 2013)”.
Ƙudirin dokar ya tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane sannan kuma ya ba da umarnin ƙwacewa da rushe dukiyoyin da ake yin amfani da su wajen aikata laifukan.
A cewar gwamnan, gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin tsaro, kisan gilla da kuma garkuwa da mutane ba.
“Na ɗauki batun rashin tsaro da muhimmanci kuma ba zan karkatar da ƙa’idar ba sai dai a yi amfani da su sosai, sabuwar dokar jihar ta ba mu damar rusa kadarorinsu da ƙwace musu filayensu.
“Za mu kawo masu garkuwa da mutane a gaban jama’a, mu kashe su domin mu nuna muhimmancinmu a kan dokokin da Majalisar Edo ta riga ta yi, ba zan ji tsoron sanya hannu a kai ba,” in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga kowa da kowa da su ba gwamnatinsa haɗin kai don tabbatar da tsaron jihar, yana mai cewa “tsaro aikin kowa ne ba na hukumomin tsaro kaɗai ba”.