✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane

An kama wadanda ake zargin ne biyo bayan sahihan bayanai game da shirin yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Eket.

Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da yin garkuwa da wasu mutane a jihar kwanan nan.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Timfon John ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Uyo, inda ya ce an kama su ne biyo bayan sahihan bayanai game da shirin yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Eket.

John wanda ya bayyana cewa mace ɗaya tilo a cikin waɗanda ake zargin ba ’yar Najeriya ba ce, ya bayyana cewa an ƙwato wata mota ƙirar leɗus da wayoyin hannu guda biyar daga hannun waɗanda ake zargin.

“A bisa wannan bayanin, jami’an rundunar sun tattara kadarori, inda suka kama wani mutum mai suna Joseph Alafia, a Garin Oron a ranar 6 ga Mayu, 2025. Wannan kamun na farko ya ƙara kai samame wurare biyu a Afia Nsit Eket.

“Waɗannan samamen da rundunar ’yan sandan ta gudanar tare da haɗin guiwa sun yi nasarar cafke wasu mutane kamar haka: Oyibo Ayibakumo Brown, namiji ɗan Jihar Bayelsa, Wisdom Harry, namiji ɗan Jihar Ribas, Afanye Igonikon, namiji dan Jihar Ribas, Dare Olaniyi, namiji ɗan Jihar Ogun, da ke zaune a garin Port Harcourt,  Jihar Rivers da kuma Tita Mercy Masume mace ’yar ƙasar Kamaru.

“A yayin samamen, hukumomi sun gano motar Lexus RX 300 mai lamba KMR 491 AE mai launin toka, waɗanda ake zargin ana amfani da su wajen yin garkuwa da mutane, tare da wayoyin hannu guda biyar.

“Waɗanda aka kama ana kyautata zaton suna da alaƙa da sace-sacen da aka yi a Eket na baya-bayan nan, kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike mai zurfi.

“Kwamishanan ’Yan sanda, CP Baba Mohammed Azare fsi, ya yaba da yadda jami’an ’yan sandan suka yi taka-tsan-tsan da ɗaukar matakin da suka ɗauka na samun nasarar kamen.