Wani bincike da aka gudanar a kasar Amurka ya gano cewa da dama daga ciki matan da ke karatu a manyan makarantun kasar su kan haihu kafin su yi aure.
Binciken, wanda waniFarfesa a fannin ilmin zamantakewa, Andrew Cherlin, ya gudanar ya gano cewa ana kara karuwar yaran da dalibai mata da ke karatu a manyan makarantu ke haifa kafin su yi aure.
Farfesan ya ce ’yan mata masu shekaru tsakani 30 zuwa 38 kan haifi dan su na farko ne kafin su yi aure.
Ya kara da cewa a da, yawan mata ’yan makarantar da ke haihuwa ba tare da aure ba ba shi da yawa amma a yanzu kuwa abin ya wuce kima.
Farfesa Cherlin ya ce binciken nasa ya gano hakan ne ta hanyar amfani da bayanan alkaluma na ma’aikatar Kididdigar Matasa ta Kasar da kuma Ma’aikatar Binciken Kasa na Karuwar Iyali.
An dai wallafa rahoto ne a mujallar bincike ta Cibiyar Kimiyya ta kasar Amurka.