A kasar Indiya, yawan mutanen da annobar COVID-19 ta kashe ya zuwa ranar Juma’a ya haura 400,000, lamarin da ya sa ta zama kasa ta uku da cutar ta fi kassarawa a duniya bayan Amurka da Brazil.
Kusan rabin mutanen dai sun rasu ne lokacin da cutar ta sake dawowa a karo na biyu a watannin Afrilu da Mayu, inda ta kusan durkusar da harkar lafiyar kasar.
- Tallafin Mai zai iya lashe N900bn a 2022 – Minista
- Ruwan sama zai iya jawo yawan hatsarin jiragen sama a bana – NEMA
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Ma’aikatar Lafiya ta Kasar ta sanar da karin mutane 853 da suka rasu sakamakon cutar, wanda hakan ya kawo jimlar wadanda ta kashe zuwa 400,312.
Kazalika, sama da karin mutum 46,000 ne suka kamu da cutar a cikin kwana dayan, alkaluman da suka sa kasar mai mutane sama da biliyan daya ta sami sama da mutum miliyan 30 da suka kamu da ita.
Sai dai a cikin kwanaki 39 da suka gabata, kasar ta sanar da mutuwar sama da mutum 100,000, tun bayan da alakaluman suka rika tashin gwauron zabo daga 24 ga watan Mayu.
Amma duk da haka, masana sun ce adadin ya zarce haka matuka saboda gwamnati ba ta kirga masu cutar kamar yadda ya kamata.
A yanzu dai babban kalubalen kasar shi ne samar da rigakfi ga al’ummar kasar sama da biliyan daya a daidai lokacin da cutar ke barazanar sake bulla a karo na uku.
Ya zuwa yanzu dai, kimanin kaso 4.5 cikin 100 na adadin mutanen kasar ne aka yi musu rigakafin. (NAN)