Kawo yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya haura 100,000 tun bayan bullar a kasar.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar cewa karin mutum 1,024 sun harbu da cutar a ranar Lahadi, lamarin ya kara yawan masu cutar zuwa 100,087.
- Sarkin Zazzau ya nada sabon Iyan Zazzau
- Ganduje zai ba Kwankwaso sarautar mahaifinsa
- Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda Tambari Yabo ya rasu
- Hamar: Kabilar da mata ke shan duka kafin a aure su
NCDC ta ce zuwa yanzu mutum 1,358 ne cutar ta coronavirus ta yi ajalinsu, duk da cewa wasu 80,030 sun warke daga gare ta.
Alkaluman NCDC na rahar Lahadin sun nuna Jihar Legas ce aka fi kamuwa da cutar a ranar inda mutum 653 suka harbu a ranar kadai.
Najeriya ita ce kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, da mutum sama da miliyan 200, ita ce a matasyi na takwas wurin yawan masu cutar a nahiyar.
Jerin kasashen da cutar coronavirus ta fi kamari a nahiyar su ne: Afirka ta Kudu, Morocco, Tunisia, Masar, Habasha, Libya, Algeria sannan Najeriya.
A makonni takwas da suka gabata dai ana a samun karuwa masu kamuwa da cutar wadda ake kara nuna damuwa game da bazuwarta a karo na biyu.