Wasu alkaluman bincike da aka wallafa ranar Litinin sun gano cewa yawan haihuwar ’ya’ya maza ya ragu sosai a shekarar 2020 a kasar Koriya ta Kudu.
Binciken na zuwa ne a daidai lokacin da bincike ke nuna cewa yawan son ’ya’ya maza na karuwa a kasar.
Binciken ya kuma yi harsashen cewa akwai yuwuwar nan da 2029 adadin matan ya zarce na maza, muddin aka ci gaba da tafiya a tsarin da ake kai yanzu.
Alkaluman dai sune mafi karanci tun da aka fara binciken a shekarar 1990.
A kasar dai, yawan maza ya haura na mata nesa ba kusa ba sakamakon yadda mutane suka fi son ’ya’ya mazan, ko da yake tun da aka sami kaiwa kololuwar yawan mazan a 1990, tazarar da ake samu ta dan ragu matuka.
Kasar dai a ’yan shakarun nan na fama da kalubalen da suka shafi karancin haihuwa da kuma yawan tsofaffi fiye da yara kanana.
Ko a shekarar 2020 sai da aka sami rahoton raguwa a yawan jama’ar kasar bayan wani bincike ya gano cewa yawan wadanda suke mutuwa ya haura wadanda ake haihuwa.