✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yawan dalibai mata ya haura na maza a Kano — Kwamishina

An gudanar da shirin ne a makarantun Firamare 300.

Yawan dalibai mata a makarantun firamaren ya zarce na dalibai maza yanzu haka a jihar Kano, a cewar Kwamishinan Ilimi na jihar, Ya’u Abdullahi ’Yanshana.

Kwamishinan ya fadi haka ne a wani taron biki na rufe shirin gangamin sa ’ya’ya mata a makaranta na GEP-3  da aka yi a jihar a ranar Litinin.

’Yanshana ya dangana karuwar dalibai mata a makarantun ga shirin gangamin sa yara mata a makaranta kan yadda aka mayar da hankali a wasu kananan hukumomin da ke shiyoyi uku na siyasa na jihar.

Sannan ya ce, alkaluman da suka nuna yawan dalibai matan da ke karatu ya karu daga miliyan 1.9 a cikin jimillar miliyan 3.8 a shekarar 2017/2018, zuwa miliyan 2.1 daga cikin miliyan 3.9 na shekarar 2019/2020.

Kwamishinan ya kuma ce, sakamakon kidayar makarantu na shekara-shekara da ake gudanarwa, kidayar shekarar 2017/2018 ya nuna cewa, adadin yawan daliban da ke makarantun Firamare 3,807,588  a cikinsu 1,978,884 mata ne.

A kuma shekarar 2019/2020, a cikin adadin dalibai 3,933,572, mata sun kai 2,050,309, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 96.5 na shigar mata makaranta da kuma tabbatuwarsu a karatu a jihar.

Kwamishinan ya ce wannan gagarumar nasara ce da aka samu da taimakon Asusun Kula da Ilimin Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, wadanda suka yi aiki a kananan hukumomin Nassarawa da Ungogo da Gwale da Municipal da Sumaila da kuma Dambatta.

Aminiya ta ruwaito cewa an gudanar da shirin ne a makarantun Firamare 300 da kuma makarantun Islamiyyah 420 na jihar.