✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaushe tsufa zai hana Cristiano Ronaldo rawar gaban hantsi?

Shi ne Kyaftin din Portugal kuma yanzu haka yana tare da Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya.

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, wanda shi ne Kyaftin din Kasar Portugal da Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya ya zarce dukkan ’yan kwallon duniya a zura kwallo a shekarar 2023.

Dan wasan ya kare shekarar da kwallo 54 ne a ragar kungiyoyi da kasashen da ya ragargaza a shekarar 2023.

Tabbatar da samun wannan nasarar tana kunshe ne a wani rahoton Kididdiga ta Kundin Bajintar Kwallon Kafa (IFFHS), inda a rahoton aka bayyana dan wasan a matsyain wanda ya fi zura kwallo a bara a hukumance a duniya.

Abin mamaki shi ne yadda dan wasan, wanda a yanzu haka yake da shekara 38 a duniya, ya zarce fitattun matasan ’yan wasa irinsu Kylian Mbappe na Kungiyar PSG da kasar Faransa wanda ya zura kwallo 52 da Haaland na Kungiyar Manchester City da kasar Norway wanda ya zura kwallo 50 da Harry Kane na kungiyar Bayern Munich da kasar Ingila wanda shi ma ya zura kwallo 52.

Wannan ya sa ake mamakin ganin duk da shekarunsa, Ronado yana ci gaba da fafatawa da matasan ’yan wasan, wadanda ake cewa su ne za su gaje shi, shi da Messi, wadanda suka dade suna jan zarensu a harkar tamaula.

A baya, an yi zaratan ’yan wasa, tun lokacin su Johan Cruyff da Michael Platini da su Pele da Mardona da sauransu.

Har zuwa lokacin su Zinedine Zidane da su Ronaldo na Brazil da Figo da Ribaldo da suransu.

Amma a tarihin kwallo ba a taba samun wadanda suka dade suna zamani ba kamar Ronaldo da Messi musamman a shekara 15 zuwa 20 da suka gabata domin da wuya a ga dan kwallo ya yi shekara 15 tauraronsa bai dusashe ba.

Wane ne Ronaldo?

Cristiano Ronaldo dos Santos Abeiro wanda aka fi sani da Cr7 an haife shi ne a ranar 5 ga Fabrairun 1985 a Tsibirin Madeira da ke kasar Portugal.

Shi ne Kyaftin din Portugal kuma yanzu haka yana tare da Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya.

Ya fara taka leda a Kungiyar Sporting CP da ke Portugal duk da cewa kafin nan ya samu tsaiko lokacin yana dan shekara 15, inda ya yi fama da matsalar cutar bugun zuciya.

A shekarar 2003 sai ya koma Manchester United yana dan shekara 18, inda ya lashe Kofin Kalubale (FA) a shekarar farko.

Sannan ya lashe Kofin Zakarun Turai daya da Firimiya ta Ingila sau 3 da sauransu.

A shekarar 2009 ya koma Real Madrid, inda ya lashe kofi 15, ciki har da La Liga 2, Copa del Rey 2 da Kofin Zakarun Turai 4, sannan ya zama Gwarzon dan Kwallon Duniya sau hudu a kulob din, inda ya zama yana da jimilla guda biyar da guda daya da ya lashe a Manchester United.

Sannan ya koma Juventus, inda can ma ya lashe Kofin Seria A, da Supercoppa Italiana, sannan ya lashe kyautar dan wasan da ya fi taka leda da wanda ya fi zura kwallo a kakarsa ta biyu.

A gida kuma, shi ya jagoranci kasar Portugal wajen lashe Kofin Nahiyar Turai, sannan shi ne ya fi buga wasa, sannan ya fi zura kwallo a tarihin tamaular kasar da sauransu.

Bayan komawarsa Manchester United daga Juventus, sai abubuwa suka fara tabarbare masa, musamman inda Kocin Man U, Ten Hag ya fara ajiye dan wasan a benci, wanda hakan ya kawo musu sabani, har ya bar kungiyar.

Aminiya ta ruwaito yadda dan wasan ya yi watanni a kasa ana neman kungiyar da zai koma a Turai, inda ana cikin hakan aka fara batun zai koma Saudiyya da taka leda.

Sai dai tun bayan komawarsa Al Nassr ta Saudiyya, fitattun ’yan wasa suka bar Turai, inda suka bi shi, suke fafatawa a can.

Da farko zuwansa can ne aka fara cewa ta kare masa, kasancewar ana cewa ya koma gasar ’yan dagaji, amma bin sa da fitattun ’yan wasa suka yi, sai ya sa gasar ta kara samun daukaka.

Bayan samun wannan nasara ta doke fitattun matasan ’yan wasa wajen zura kwallo a kakar bara, dan wasan ya bayyana cewa yana da burin ganin ya sake doke matasan ’yan wasan a bana kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da kafafen watsa labarai.