✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta hana madugun adawar Senegal Ousmane Sonko tsayawa takara

A watan Yulin bara ne jam’iyyar adawar kasar Senegal ta tsayar da Ousmane Sonko takara.

Kotun Kolin Senegal a wannan Juma’ar ta yanke hukuncin haramta wa madugun adawar kasar, Ousmane Sonko tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben da ke tafe a watan Fabrairu.

Bayanai sun ce kotun ta yi watsi da daukaka karar da Sonko ya yi, inda ya ke kalubalantar hukuncin daurin watanni 6 da aka zartas masa a baya kan laifin kazafi da bata suna, matakin da kai tsaye ke hana shi damar tsayawa takarar zaben shugaban kasa.

Tun daga shekarar 2021 ne Ousmane Sonko mai shekaru 49 ya ke fama da mabanbantan tuhume-tuhume a gaban kotu, lamarin da ya haddasa nakasu a shirinsa na tsayawa takakarar zaben shugaban kasa.

Haka zalika, wannan tuhume tuhume sun haddasa yamutsi da tashe-tashen hankula da suka kai ga rasa rayuka, jikkatar wasu da ma kame wani adadi cikin masu zanga-zangar kalubalantar matakin.

Bayan zaman kotun da aka faro tun a yammacin jiya Alhamis, a yau Juma’a gamayyyar alkalan da suka jagoranci zaman shari’ar sun yi watsi da daukaka karar ta Sonko tare tsayawa kan hukuncin na farko da ke tabbatar da daurin watanni 6 kansa game da kazafin da bata suna.

Baya ga wannan tuhuma, Sonko na kuma fuskantar wasu mabanbantan tuhume-tuhume ciki har da zargin fyade da cin amanar kasa.

Wadannan matakai dai kai tsaye sun haramta masa damar tsayawa takara, lura da cewa karkashin dokokin Senegal babu wanda zai iya tsayawa takarar zabe matukar akwai tuhume-tuhumen da kotu ke tsaka da shari’a akansu.

A jawabinsa na kai tsaye ga babban gidan rediyon Senegal jim kadan bayan kammala zaman kotun da safiyar yau Juma’a, lauyan masu shigar da kara, El Hadji Diouf ya bayyana samun gagaruma nasara wajen dakile Sonko daga tsayawa takarar zaben.

A bangare guda lauyan da ke kare Sonko, Cire Cledor Ly ya shaida wa manema labarai cewa hukuncin ba zai karya musu gwiwa ba, domin kuwa za su ci gaba da fafutuka wajen ganin an tabbatar da adalaci ga Ousmane Sonko tare da sahale masa damar tsayawa takara.

Babu dai wata alamar tashin hankali har zuwa yanzu a Senegal, sai dai jami’an tsaro na cikin shirin ko ta kwana lura da dimbin magoya bayan da Sonko ke da shi a sassan kasar ta Yammacin Afirka.

Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Yulin bara ne jam’iyyar adawar kasar Senegal ta tsayar da Ousmane Sonko takara a zaben da ke tafe cikin watan Fabarairun shekarar nan.

Babbar jam’iyyar adawar Senegal ce ta ayyana shugabanta Sonko a matsayin dan takararta, tana mai watsi da tambayoyi game da cancantar sa.

A wancan lokacin dai an zabi Sonko a matsayin dan takarar jam’iyyar PASTEF-Patriots na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024.

Ousmane Sonko ya samu karbuwa a tsakanin matasan Senegal da ke fama da rashin gamsuwa da gwamnati mai ci, ta hanyar yin kamfe mai zafi a kan shugaba Macky Sall, na nuna shi a matsayin mai cin hanci da rashawa kuma mai mulkin kama-karya.