Kotu ta yanke wa wani dan kasuwa a Kaduna daurin shekara shida a gidan yarin kan yi wa wani abokin harkarsa damfara ta Naira miliyan 20.
Babbar Kotu Jihar Kaduna ta kuma umarci mai laifin ya mayar wa mai kudin Naira miliyan 20 da ya ba shi domin harkar sayar da motoci.
- DAGA LARABA: Yadda Iyaye Ke Lalata Da ’Ya’yan Cikinsu
- Kamfanin jiragen sama ya fara zirga-zirga daga Abuja zuwa Jigawa
Alkalin kotun kotun ya ba da umarnin kara wa mai laifin zaman wakafi na shekara daya idan ya kasa biyan kudaden.
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan dan kasuwan ya amsa laifin ya kuma nemi afuwarta.
Lauyan EFCC ya shaida, EK Garba, shaida wa kotun cewa, a shekarar 2020 dan Kasuwar da aka gurfanar ya yaudari wani mai suna Jamil Hassan ya ba shi Naira miliyan 20 da sunan zai fara sana’ar sayar da motoci.
Sai dai maimakon haka, sai ya karkatar da kudaden ya yi ta sha’anin gabansa da su.