✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a yi jadawalin wasan kwata-fainal a gasar cin kofin Champions League

A yau Juma’a ne da misalin karfe 12 na rana ake sa ran Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai za ta fitar da jadawalin…

A yau Juma’a ne da misalin karfe 12 na rana ake sa ran Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai za ta fitar da jadawalin wasan kwata-fainal na jadawalin gasar zakarun kulob-kulob na Turai a hedkwatar Hukumar da ke Nyon na kasar Suwazilan.

A shekaranjiya Laraba ne dai kulob din FC Barcelona da ke Sifen da na Jubentus da ke Italiya suka kammala wasanninsu bayan sun samu nasara.
Za a kasafta kungiyoyin kwallon kafa da suka rage guda takwas ne wadanda ake sa ran za su hadu da juna a wasan gida da waje kafin a tantance wadanda za su haye matakin kusa da na karshe semi-fainal a gasar.
kungiyoyi kwallonsa kafa takwas da suka haye matakin kwata-fainal din sun hada da kulob din Real Madrid da FC Barcelona da Atletico Madrid dukkanninsu daga Sifen, sai kulob din Bayern Munich daga Jamus sai na Jubentus daga Italiya sai na Monaco da PSG daga Faransa sai FC Porto daga Fotugal.
Sai dai akwai yiwuwar kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da FC Barcelona su hadu a wasan kwata-fainal kamar yadda jadawalin ya nuna. Sannan za a yi wasannin farko ne a ranakun 5 da 6 ga watan Afrilu yayin da za a yi wasannin zagaye na biyu a ranakun 12 da 13 na watan Afrilun, 2015.
Haka kuma a ranar 24 ga watan Afrilu ne ake sa ran za a sake jadawalin wasan kusa da na karshe watau semi-fainal yayin da za a gudanar da wasannin ne a ranakun 5 da 6 ga watan Mayun wannan shekara yayin da za a yi wasannin zagaye na biyu a ranakun 12 da 13 ga watan Mayun.
A ranar Asabar 6 ga watan Yunin wannan shekarar ce ake sa ran za a gudanar da wasan karshe a filin wasa na Olympiastadion da ke Berlin na kasar Jamus.
Ana sa ran za a nuna jadawalin gasar kai tsaye ne a akwatin talabijin a sassan duniya.