A yau ne za a cin gaba da shari’ar uwa da ’ya da ake zargi da satar kananan yara suna sayarwa a Kano.
An gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban Kotun Majistare Mai lamba 37 da ke Sakatariyar Audu Bako a Kano wadda ta bayar da umarnin a tsare mata da ’yarta zuwa yau don ci gaba da shari’ar.
Tunda farko ’yan sanda ne suka yi wa matar kofar rago inda suka kame su tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Bayan karanta musu takardar tuhumar laifin satar kananan yaran, ’yar matar mai shekara 13 a duniya ta shaida wa kotun cewa ita ma ba ’yar matar ta hakika ba ce kamar yadda ake fadi, domin tarihi ya nuna cewa sato ta matar ta yi tun tana ’yar shekara uku. “A lokuta da dama idan na tambayi iyayenta, wane ne mahaifina sukan gaya min cewa su ma ba su san shi ba, domin haka kawai suka gan ta tare da ni. Kuma idan na tambaye ta sai ta ce wai mahaifina ya yi hadarin mota ya mutu,” inji yarinyar.
Yarinyar ta shaida wa kotun cewa matar tana amfani da ita ce wajen raba wa yaran da suke son sacewa alawa “Mukan rararba wa yara alawa, kuma kasancewar tana amfani da wani malami da ke ba ta magani da zarar ta ba yaran alawar suka sha shi ke nan ba za su yi kuka ba sai yadda muka yi da su,” inji yarinyar.
Ta ce, “Idan muka dauki yaran sai mukai wa Femi yaran a Legas ko kuma shi ya zo da kansa ya karba. Ni dai ban san a kan nawa ake sayar da yaro ba, duk kuwa da cewa yana ba ta kudi masu yawa.”
Lauyan da ya dauki nauyin tsaya wa yarinyar mai suna Barista Gwani ya ce ya yi haka ne saboda tausaya wa yarinyar tare da neman kyautata rayuwarta a nan gaba. “Mun fahimci cewa wacce ta sanya ta a wannan harka ba uwarta ba ce, ita ma sato ta aka yi,” inji shi.
Alkalin Kotun Mai shari’a Halima Wali ta bayar da umarnin a tsare matar a kurkuku, sannan ta damka yarinyar a Hannun Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP) tare da dage shari’ar zuwa yau.