’Yan sanda sun gano harsasai guda 500 a wata maɓoyar masu aikata laifuka da ke kusa da hanyar Bauchi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya ce an gano harsasan ne ta hanyar rahotannin sirri, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka a jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa an gano harsasan ne bayan wani kisan kai da ya faru a yankin, inda aka kashe wani da ba a gane ko wanene ba.
“Bayan samun rahoton faruwar lamarin, nan take muka fara gudanar da bincike domin gano yanayin da ya kai ga mutuwar wanda aka kashe.
- An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan sun sha ‘Kayan Mata’
- ’Yan sanda sun bankaɗo masana’antar man gyaɗa na bogi a Kaduna
“A yayin gudanar da wannan binciken ne aka samu nasarar gano waɗannan harsasan. Ina so in ba ku tabbacin cewa muna ci gaba da ƙoƙarin ganowa tare da kama waɗanda suka aikata wannan laifin tare da ƙwato makamansu.”
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba su duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen kama su.