Hedikwatar ’yan sandan Gada da ke Jihar Sakkwato ta gano wasu shanu 25 da ake zargin an sace ko kuma sun ɓace daga hannun masu su.
An gano dabbobin ne a wani dajin da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar Alhamis, bayan da hukumomin yankin suka samu labarin.
- ’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo
- Shettima zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Gabon
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an gano dabbobin ne bayan da Alhaji Muhammad Kyari ya bayar da rahoton cewa akwai shanun da suka ɓace.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hakimin Gada, Alhaji Idi ‘M, tsohon Hakimin garin Gidan Rabami da ke ƙaramar Hukumar Gada, a baya ya sanar da hukuma game da wasu baƙin shanu a wani dajin da ke kusa.
“An gano dabbobin ne a wani dajin da ke da iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni, yankin da ya shahara da sarƙaƙiya da kuma ƙalubalen tsaro a wasu lokuta.
“Rundunar ’yan sanda ta Gada ta mayar da martani cikin gaggawa, inda ta tura jami’anta zuwa wurin da aka yi nasarar ƙwato shanu 25 ba tare da wata matsala ba.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan kuɓutar da su an kai shanun zuwa hedikwatar Gada, inda ake tsare da su cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ’yan sandan ta yi kira ga masu dabbobin da suka rasa shanunsu da su ziyarci hedikwatar tare da ingantacciyar hujjar mallakar su domin tantancewa tare karɓarsu.