Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri.
An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata.
Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an gurfanar da 64 daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin Maphites, Eiye, da Aye kuma ake zarginsu da kisan gilla da aka yi kwanan nan a rikicin kungiyoyin asiri.
Kayan da aka ƙwato sun hada da bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga guda mai tashi daya, da harsashi 24.
’Yan sandan sun shawarci iyaye da su kula da ayyukan ’ya’yansu kuma sun gargadi matasa da kada su shiga kungiyoyin da ba bisa ka’ida ba wadanda ke kawo hatsari ga rayuwarsu.
Bincike na ci gaba da gudana kan sauran wadanda ake zargin.