✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano

“Rundunar ’yan sandan ta gudanar da wani samame ta hanyar fasaha da bayanan sirri, ta kama waɗanda ake zargin da wannan miyagun ƙwayoyin, biyo bayan…

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama aƙalla mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda suka hada da: Muntari Shu’aibu da Imrana Rabi’u.

A wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu waɗanda ake zargin ɗauke da ƙunshi guda shida na miyagun ƙwayoyin  Tramadol da aka ƙiyasta kuɗinsu ya haura Dala 92,000 (kimanin Naira miliyan 150m).

Bakori ya ce, “Rundunar ’yan sandan ta gudanar da wani samame ne ta hanyar fasaha da bayanan sirri, ta kama waɗanda ake zargin da wannan miyagun ƙwayoyin, biyo bayan wani rahoto da aka samu.”

Ya ƙara da cewa, kamun wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi kan magance musabbabin munanan laifuka a jihar.

Ya ci gaba da cewa, “Hakan ya biyo bayan ƙoƙarin da hukumar ke yi na daƙile ayyukan ta’addanci, waɗanda a cewarsa galibin safarar muggan ƙwayoyi ne na sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar.”

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa an miƙa waɗanda ake zargin ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa reshen Jihar Kano domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban ƙuliya.

“Wannan ya yi daidai da tsarin Sufeto-Janar na ‘yan sanda na aikin ‘yan sanda da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a tsakanin ƙungiyoyin tsaro,” in ji shi.