✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi

Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar…

Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar Bauchi.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ana tuhumar huɗu daga cikin mutanen da aikata laifin fyade, zubar da ciki da kuma mutuwar budurwa a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau.

Wakil ya ce, a ranar 4 ga Afrilu, 2025 sun samu bayanai ewa, kimanin watanni hudu da suka gabata, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun kama wata yarinya mai shekaru 18 da suka yi ta yi lalata da ita sau da yawa.

Ya ce a lokacin da suka lura tana ɗauke da juna biyu, sai suka nemi wani mutum suka ba shi naira 40,000 don ya taimaka musu wajen zubar da cikin, amma abin takaici sai aka samu matsala wanda a qarshe ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Wakil ya ce, “Bayan an yi mata allurar zubar da ciki saita fita daga hayyacinta, daga baya kuma ta kamu da rashin lafiya. Hakan ya sa danginta suka kai ta Babban Asibitin Misau, daga baya an mika ta zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare, inda hukumomin asibitin suka sanar da cewa ta mutu a lokacin da take jinya.”

Bayan samun rahoton, an kama wadanda ake zargin, inda suka amsa laifin da suka aikata tare da ambaton wasu da ke da hannu a lamarin.  Ya ce sauran wadanda ake zargin da wasu mutum huɗu suna hannun ’yan sanda ana bincike.

Bayan haka kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa laifukan da suka aikata.”