✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano

Abba Dujal ya ce yanzu haka ya shekara bakwai bai yi sallah ba.

Wani matashi, Umar Auwal, mai shekaru 20 da ya yi iƙirarin kashe mutane ya miƙa kansa ga rundunar ’yan sanda a Jihar Kano.

Matashin mai inkiyar ‘Abba Dujal’ ya ce ya miƙa kansa ga mahukunta ne sakamakon rashin samun kwanciyar hankali tun bayan ta’addancin da ya aikata a bayan nan.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon murya da kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Da yake amsa tambayoyi, Abba Dujal ya yi iƙirarin aikata manyan laifuffuka da suka haɗa da kisan kai, fashi da makami da kuma satar babur da wayoyin hannu.

Matashin ya yi iƙirarin kashe wani mutum mai suna ‘Boka’ a unguwar Sabon Gari ta Kano, inda ya sace wayarsa Infinix Hot 40i, ya kuma sayar da ita a kan N40,000.

Haka zalika, ya bayyana yadda ya kashe wani mutum a unguwar Kurna da ke Kano, inda ya arce da wayarsa ƙirar Samsung S26 da ya sayar a kan N160,000.

A Jigawa kuwa, ya ce ya kashe wani mutum a karamar hukumar Ringim tare da sace babur ɗinsa da ya sayar da shi a kan N350,000.

Abba Dujal ya ce yanzu haka ya shekara bakwai bai yi sallah ba. Sai dai ya ce an saka shi a Islamiyya amma malamin ya dawo da shi gida saboda fitinar da yake a makarantar.

A fannin karatun boko kuma, Abba Dujal ya ce ya taɓa shiga firamare amma daga nan bai ƙara gaba ba.

Ya kuma ce ya ɗan samu ilimin karatun fatiha da ’yan ƙananan surori a yayin zaman gidan yarin bayan laifin fashi da makami da suka aikata a gidan Hakimin Wudil.

Rundunar ta tabbatar da cewa a halin yanzu, an tsare matashin a sashen binciken manyan laifuffuka domin ci gaba da bincike da kuma tabbatar da gaskiyar iƙirarin da ya yi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar , CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana jin daɗinsa kan matakin da Dujal ya ɗauka na miƙa wuya.