A yau Juma’a ne ake buɗe katafaren masallaci hade da makaranta da dakin taro da na laburare da gida da rauda da aka gina wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi a garin Bauchi.
Masallaci da ake cewa da wuya a samu irinsa a nan kusa an gina shi ne da taimakon Dokta Bala Maijama’a Wunti a karkashin gidauniyarsa ta Wunti Alkhayr Foundation.
Shirye-shiryen bude masallaci ana yi ne tsakanin gidauniyoyin da Wunti Alkhayr da Mu’assasar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
- Mai Keke-Napep ya mayar da N2.4m da ya tsinta a Taraba
- Biden ya caccaki Trump kan goyon bayan Rasha a mas’alar NATO
Don share fagen bude masallacin Muassasar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta shirya Musabakar Alkur’ani karo na farko a tsakanin jihohin kasar nan a tsakanin maza da mata tun daga izu biyu zuwa biyar izu 60 da Tafsiri da Larabci.
Ana sa ran fiye da mutu, 5000 su yi Sallah a cikin masallacin, kuma ana sa ran Babban Halifan Shehu Ibrahim Nyas, Shehu Muhammadu Mahiy Nyass ne zai jagoranci Sallar Juma’a a yau.
Ana sa ran manyan malaman da za su yi jawabi sun hada da Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh El-Hussein da Farfesa Ibrahim Makari, Limamin Masallacin Kasa da ke Abuja da Sheikh Mustafa Briggs daga Ingila da Dokta Bashir Dahiru Bauchi.
Manyan bakin da ake sa ran za su halarci bude masallacin sun hada da Shugaban Bola Ahmed Tinubu, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Mai martaba Sarkin Kano da sarakunan Jihar Bauchi karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, sai Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed da zai jagoranci sauran gwamnoni, sai malamai daga kasashen Saudiyya da Maroko da Aljeriya da Senegal da Mauritaniya da Nijar da Kamaru da Chadi da sauransu.
Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da Limamin Bauchi Malam Bala Ahmad Baban’inna da sauran malamai da dama da Aminiya ta zanta da su sun yaba aikin da wannan bawan Allah ya dauki nauyin yi, inda suka roki Allah Ya saka masa da alheri.