Yau Lahadi take Sallah a Jamhuriyyar Nijar bayan da gwamnati ta sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan a kasar.
Tuni Shugaba Mohamed Bazoum ya aike da sakon ‘Barka da Sallah’ ga ilahirin al’ummar jamhuriyar Nijar a shafinsa na Tuwita, tare da addu’ar samun zaman lafiya da tsaro a kasar.
Bikin Sallah a Nijar ta sa na zuwa ne bayan da makwabciyarta Najeriya, ta ba da sanarwar cewa ba a ga watan Shawwal ba a kasar ranar Asabar, saboda haka azumi 30 za a yi..
Amiiya ta ruwaito Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ta bakin kwamitin ba da shawarwari kan harkar addinai na Majalisar Sarkin tana cewa ba ta samu rahotan ganin watan ba daga dukkan kwamitocinta.
A don haka ne ma Majalisar ta ambata ranar Litinin a matsayin ranar Sallah karamar a kasar.
Sarkin Musulmin Sa’ad Abubakar ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba, tare da yi musu barka da Sallah.
Wasu kasashen Musulmi na duniya dai irinsu Saudiyya su ma sun fitar da makamanciyar wannan sanarwar ta rashin ganin watan a ranar Asabar.