✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau Liverpool za ta karbi bakuncin Chelsea a Anfield

Liverpool tana matakin farko a kan teburin Firimiyar da maki 48, bayan karawa 21.

A Yammacin wannan Larabar Liverpool za ta yi karon-batta da Chelsea a wasan mako na 22 na gasar Firimiyar Ingila a Anfield.

Masu ruwa da tsaki a fagen tamaula na hasashen cewa Liverpool ce za ta doke Chelsea a wasan la’akari da yadda ta fi samun rinjayen nasara a haduwarsu ta baya bayan nan.

Haka kuma, an fi jingina wa Liverpool nasara sakamakon kasancewarta mai masaukin baki kuma alkaluma na tarihi suka nuna cewa kociyanta, Jurgen Klopp yana da sa’a a kan kociyan Chelsea, Mauricio Pochettiino.

Liverpool tana matakin farko a kan teburin Firimiyar da maki 48, bayan karawa 21.

Chelsea ma wasa 21 ta buga, tana mataki na tara da maki 31 a babbar gasar tamaular ta Ingila.

Liverpool, wadda take ta daya a kan teburin Firimiyar ta kai wasan karshe a Carabao Cup da samun gurbin mataki na biyar a FA Cup.

Haka kuma kungiyar ta Merseyside ta kai zagaye na biyu a gasar zakarun Turai ta Europa League.

A watan Agustan bara kungiyoyin sun tashi 1-1 a Stamford Bridge, inda Luis Diaz ya fara ci wa Liverpool kwallo daga baya Chelsea ta farke ta hannun Axel Disasi.

A makon jiya ne kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya sanar cewar zai ajiye aikin horar da kungiyar a karshen kakar nan.

Hakan ne ya sa kyaftin ɗin kungiyar Virgil van Dijk ya ce bai san makomarsa ba a Anfield da zarar ɗan kasar Jamus din ya yi murabus.