✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 91 aka kashe a rikicin Mangu —Shugaban Matasa

An jikkata wasu 158, aka kona gidaje 114 da wuraren ibada a rikicin makon jiya

Shugaban Kungiyar Matasan Mwaghavul na Kasa, Kwamared Sunday Dankaka, ya ce an mutane 91 aka kashe, sannan aka jikkata wasu 158 a rikicin da ya barke a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato a makon jiya.

Sunday Dankaka ya shaida wa manema labarai a Jos a ranar Talata cewa wadanda aka kashe sun hada da mata 42, yara 37 da maza 12; aka kona gidaje 114, da masallatai 9 da coci 15.

Darakta na kungiyar Equity International Initiative, Chris Iyama, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen tallafa wa al’ummomin da ’yan bindiga suka kai wa hari a kananan hukumomin Mangu da Bokkos na jihar.

Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta kwato su tare da tabbatar da duk filayen noma da gidajen da masu su suka tsere suka bari, domin duk manoman da suka bar filayen kakanninsu su samu kwanciyar hankali su koma yankunansu da gonakinsu.

“Muna kuma kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa da ta kara kaimi wajen bayar da agaji ga daukacin al’ummomin da abin ya shafa,” in ji shi.