✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe jagoran ’yan ta’adda sun ceto mutane 20 a Zamfara

Sojoji lalata duk sansanonin ’yan ta'adda da aka kai wa samame

Sojoji sun kashe wani jagoran ’yan bindiga suka ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

Kakakin Rundunar Operation Hadarin Daji, Kyaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojoji sun kashe jagoran ’yan bindiga mai suna Sainaje a yayin musayar wuta a samamen da suka kai maboyar ’yan ta’addan.

Ya bayyana cewa mata 14 da maza huɗu an ceto su ne a yankin hukumomin Zurmi da Birnin Magaji, sai wasu biyu an ceto su ne a kan hanyar Isa zuwa Shinkafi.

Kyaftin Yahaya Ibrahim ya ce an yi nasarar ceto mutanen ne a samamen da sojoji suka kai ranar Litinin a maboyar ’yan ta’adda a kauyukan Rukudawa, Dumburum, Tsanu, Birnin Tsaba, Magare danke kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji.

Ya bayyana cewa an lalata duk sansanonin ’yan ta’adda da aka kai wa samame kuma sun mika duk wadanda ake ceton ga hukumomin da suka dace.