Wasu fusattun matasa sun ƙone wata gonar kiwon kaji a yankin Etoo Baba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato bisa zargin kashe wani mai gadi da ke aiki a gidan gonar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa fusatattun matasan sun kuma yi awon gaba da tsuntsaye kafin su cinna wa gidan gonar wuta da safiyar Talata.
- An tsinci gawar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Oyo
- Rikicin Kabilanci Ya Yi Ajalin Mutum 2 A Binuwai
Wani mazaunin unguwar, Mista Paul Alhassan wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce matakin da matasan suka ɗauka ya haifar da tashin hankali a ciki da wajen al’umma.
Ya ce “Gobarar ta ƙone komai ciki har da motocin da aka ajiye a harabar gidan gonar, daga nan kuma ta bazu zuwa wani gini na wani maƙwabci.
“Abin da na ji shi ne matasan sun fusata ne saboda wani mai gadi da ke aiki a gonar da mamallakinta ya riƙa duka har ya kai ga ajalinsa bayan an zarge shi da satar ƙwai a gonar.
“Don haka bayan mai gadin ya mutu, sai matasan suka zargi ɗan mai gonar da kashe shi, daga nan kuma sai matasan suka fusata suka ƙona gonar gaba ɗaya.
“Kazalika matasan sun ƙona gidan mai kajin,” in ji Al Hassan.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wasu jami’an hukumar kashe gobara ta jihar sun isa inda gonar take domin daƙile bazuwar wutar zuwa wasu wurare.
A halin da ake ciki, an tura jami’an tsaro yankin domin tarar hanzarin abin da ka iya zuwa ya komo.