A safiyar yau Litinin ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa a cibiyar tattara sakamakon zaben na kasa da ke Abuja.
A ranar Lahadi da dare ne dai Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya dage tattara sakamakon bayan karbar na Jihar Ekiti, wanda baturen zaben jihar, Farfesa Ayobami, ya gabatar.
- Fasinjan jirgin kasan Abuja-Kaduna ya ci zaben Majalisar Tarayya
- NAJERIYA A YAU: Zaben Shugaban Kasa Ya Bar Baya Da Kura
Farfesa Yakubu, ya ce za a ci gaba da aikin da misalin karfe 11 na safiyar Litinin, lokacin da ake fata an kawo sakamakon zaben sauran jihohi 35 da kuma birnin tarayya.
Sakamakon zaben shugaban kasa na Jihar Ekiti ya nuna cewa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ya samu kuri’a 210,494, Atiku Abubakar na PDP 89,554, Peter Obi na LP 11,397 sai Rabiu Kwankwaso na NNPP kuri’a 264.
A ranar Asabar aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda sa’o’i kadan kafin ranar shugaban hukumar ya ba da tabbacin cewa a wannan karon hukumar za ta fitar da sakamakon zabon a kan kari ba kamar yadda aka yi a baya ba.
Idan za a iya tunawa dai, a zaben shugaban kasa na 2019, sai a ranar Talata INEC ta sanar da wanda ya ci, bayan kammala zaben a ranar Asabar.