✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau Iheanacho zai sanya hannu a kulob din Manchester City

dan kwallon Golden Eaglets Kelechi Iheanacho ya samu amincewa daga kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi kuma tuni ya tafi Ingila don…

dan kwallon Golden Eaglets Kelechi Iheanacho ya samu amincewa daga kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi kuma tuni ya tafi Ingila don kulla yarjejeniya da kulob din Manchester City a yau Juma’a.
Iheanacho, shi ne na biyu a wajen zura kwallaye a raga a gasar cin kofin duniya na matasa da aka yi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a watan jiya.
Idan za a tuna a labarin da Aminiya ta buga kimanin makwanni uku da suka wuce an nuna mahaifin Iheanacho yana nemansa ruwa a jallo saboda bai san takamaiman inda ya shiga ba.  An yi ta rade-radin dan kwallon ya tsallake zuwa Turai ne don sanya hannu a wani kulob da ba a ambata ba.
Sai dai a yanzu ta tabbata dan kwallon tare da amincewar mahaifinsa ya samu tafiya Ingila ne don ya sanya hannu a kulob din Manchester City.
Masana harkar kwallo suna ganin bai dace dan kwallon ya sanya hannu a kulob din City ba ganin cewa da wuya ya rika buga kwallo a kan kari saboda zaratan ’yan kwallon da kulob din yake ji da su.
Rahoton da ke fitowa daga kulob din City ya tabbatar idan kulob din ya kulla yarjejeniya da Iheahancho akwai yiwuwar ya tura shi kasar Ghana don ya cigaba da samun horo a sansanin horar da matasa na kulob din City da ke can kafin daga bisani idan ya goge kulob din ya mayar da shi Ingila don ya cigaba da yin wasa a matakin manya.