✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau da gobe za a buga wasan kwata-fainal

A cigaba da gasar cin kofin duniya a Brazil a yau Juma’a da kuma gobe Asabar ne&nbsp kasashe takwas da suka kai matakin kusa da…

A cigaba da gasar cin kofin duniya a Brazil a yau Juma’a da kuma gobe Asabar ne&nbsp kasashe takwas da suka kai matakin kusa da na karshe watau kwata-fainal za su fafata.
Faransa za ta kece raini ne da Jamus a wasan farko da zai gudana da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya yayin da a wasa na biyu kuma za a yi wasa a tsakanin mai masaukin baki Brazil da Kolombiya da misalin karfe tara na dare.
A gobe Asabar kuma da misalin karfe biyar na yamma za a fatata ne a tsakanin kasar Ajantina da ta Beljiyam yayin da wasa na biyu kuma zai gudana ne a tsakanin kasashen Holan da Costa-Rica da misalin karfe 9 na dare.
Duk kasashen da suka samu nasara ne za su haye matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.