✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Tinubu: Yau Atiku da Obi za su san matsayinsu a kotu

Atiku da Peter Obi na neman kotu ta soke zaben Tinubu, inda kowannensu ke son a ayyana shi a matsayin zababen shugaban kasar Najeriya

A yayin da Shugaba Bola Tinubu ke cika shekara 100 a kan mulki a yau din nan ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2023 za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke kalubalantar nasararsa a zaben.

Kotun da ke zamanta a Abuja ta sahale wa kafofin yada labarai nuna zaman kai-tsaye, wanda ba kasafai aka saba yi ba.

Baban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu a zaben, tare da Peter Obi na jam’iyyar LP da ya zo na uku ne suka shigar a karar.

Atiku da Peter sun nuna kwarin gwiwar samun nasara a shari’ar, inda kowannensu ke neman kotun ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

A safiyar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023 ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar 25 watan da kuri’u mafi rinjaye — 8,794,726.

Tun kafin a kai ga sanar da sakamakon zaben na karshe dai jam’iyyun PDP da LP da wasu suka yi fatali da shi, bisa zargin magudi da saba dokar zabe, inda suka ce za su shigar da kara a gaban kotu.

Sai dai kuma daga cikin jam’iyyu 18 da ake da su a Najeriya, 11 sun nesanta kansu da boren da PDP ta jagoranta na ficewa daga cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a Abuja.